fidelitybank

An kashe manoma biyu a Benue a wani sabon rikici

Date:

Rahotanni sun ce an kashe manoma biyu a wani sabon hari da aka kai a unguwar Ikyungwa Tombo, kusa da al’ummar Ayilamo a karamar hukumar Logo a jihar Benue.

Aminiya ta tattaro cewa, lamarin ya faru ne a ranar Litinin da karfe 5 na yamma yayin da su biyun ke dawowa daga gonakin su.

An bayyana sunayen wadanda suka mutun a matsayin Bem Uhembe da Mungwa Zuzu, dukkansu ‘yan kauyen Tse Ibor ne da ke komawa garin Ayilamo bayan sun yi aikin gonakinsu, saboda zargin wasu da ake zargin makiyaya ne suka kwace matsugunan su.

Mutanen yankin sun ci gaba da cewa an ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na Ayilamo.

Shugaban karamar hukumar, Aber Terse, ya tabbatar wa wakilinmu ta wayar tarho cewa, wadanda suka mutu – wata mace da namiji – an yi musu dirar mikiya tare da kashe su bayan sun bar gonakinsu da yammacin ranar Litinin.

Aber ya zargi makiyayan da laifin kisan mutanen biyu sakamakon mamayar unguwar Tombo, wani wurin noma, wanda wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton makiyaya ne ke ci gaba da kai musu hari tun a shekarar 2016.

nigerianewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp