fidelitybank

An kashe makiyaya 10,000 cikin shekara 7 a kasar nan – Miyetti Allah

Date:

Ƙungiyar kare al’adun Fulani a Najeriya ta Miyetti Allah ta ce an kashe makiyaya aƙalla 10,000 tare da raba wasu miliyan biyu da muhallansu a faɗin ƙasar cikin shekara bakwai da suka wuce.

Bayanan sun fito ne bayan wani taro kan tsaro da ƙungiyar ta shirya tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Northern Consensus Movement (NCM) ta ‘yan Arewa sakamakon matsalolin tsaro da suka ce Fulani na fuskanta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito ranar Asabar.

Cikin wata sanarwar bayan taro a ranar Juma’a, ƙungiyar ta ce daga 2015 zuwa yanzu makiyaya da dama sun fuskanci matsaloli, inda aka sace ko kashe dabbobi fiye da miliyan huɗu.

“Yi wa Fulani baƙin fenti da nuna musu tsana da kuma rura wutar ƙabilanci a kan su da kafofin yaɗa labarai ke yi ka iya kaiwa ga kisan ƙare-dangi,” in ji sanarwar.

“Ayyukan ƙungiyoyin Indigenous People of Biafra (IPOB)/Eastern Security Network (ESN) da ’Yan-Sa-Kai sun ƙara ta’azzara lamarin da kuma kawo barazana ga zaman Najeriya ƙasa ɗaya.”

Ana yawan zargin wasu ‘yan ƙabilar Fulani da aikata fashi da garkuwa da mutane musamman a jihohin arewa maso yammacin Najeriya, abin da shugabanni da ƙungiyoyin ƙabilar ke musantawa.

nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp