Akalla ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka hudu ne aka kashe a Najeriya da ke aikin jin kai a jihar Anambra.
Jaridar DAILY POST ta bayar da rahoton cewa, an kashe su ne a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa motar su hari a ranar Talata.
Lamarin ya faru ne a yankin Amiyi/Eke Ochuche da ke karamar hukumar Ogbaru a jihar.
An fahimci cewa maharan sun mamaye wurin da mazauna wurin ke jiran jinya daga jami’an UNICEF.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga ya fitar, ya ce, “Jami’an tsaro na hadin gwiwa sun fara aikin ceto a karamar hukumar Ogbaru, bayan wani hari da aka kai kan ayarin motocin ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka a yau 15 ga watan Mayu. 2023 da 3:30 na yamma tare da Atani, Osamale road.
‘Yan ta’addan sun kashe jami’an ‘yan sanda biyu, da ma’aikatan ofishin jakadancin biyu, tare da kona gawarwakinsu tare da motocinsu.
Ikenga ya nace cewa “babu wani dan Amurka da ke cikin ayarin motocin”.