Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da kisan wani jagoran Boko Haram mai suna Bakura, a yankin Tafkin Chadi, inda ƙasar ke iyaka da Najeriya da Chadi da Kamaru.
A wata sanarwa da sojojin suka fitar a ranar Alhamis, an kashe Bakura ne yayin wani aikin soji a wani tsibiri a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Nijar a makon da ya gabata.
Bakura dai ya jagoranci wani ɓangare na ƙungiyar Boko Haram wadda ke biyayya ga tsohon shugaban ƙungiyar, Abubakar Shekau, inda ya ƙi shiga reshen abokan hamayyar su na ISWAP inda ya koma tsibirin da ke gefen Nijar na tafkin tare da mayaƙansa.
Rikicin Boko Haram ya fara ne tun 2009 a arewa maso gabashin Najeriya, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 40,000 sannan ya tilasta wa sama da miliyan biyu tserewa daga gidajensu.
Rikicin ya kuma bazu zuwa ƙasashen makwabta, inda Nijar ta fuskanci hare-hare na farko daga kungiyar a Bosso a 2015.
Sojin Nijar sun ce an kai harin ne da jirgin yaki a safiyar 15 ga Agusta, inda suka bayyana cewa sun harbi Bakura sau uku a matsayinsa na shugaba a Shilawa.
Sunan asali na Bakura shi ne Ibrahim Mahamadu, mai kimanin shekara 40 a duniya kuma É—an asalin Najeriya ne.
Ya shiga Boko Haram sama da shekaru 13 da suka gabata, sannan ya karɓi shugabancin kungiyar bayan mutuwar Shekau a watan Mayu 2021