Kungiyar likitoci a Sudan, ta ce kusan farar hula 100 aka kashe a faɗan da ake yi tsakanin sojojin gwamnati da waɗanda ba na gwamnati ba.
Kungiyar likitocin ta yi gargaɗin cewa asibitoci na fama da rashin kayan aiki a birnin Khartoum, tare da yin kira ga sojin gwamnati da na RSF da su mutunta dokokin yaki.
Wakilin BBC ya ce an ɗan tsagaita buɗe wuta ta sa’o’i kaɗan da MDD ta bukata, domin kai ɗaruruwan waɗanda suka jikkata asibiti, sai dai hakan bai yi tasiri ba sakamkon ci gaba da gwabza faɗa da ɓangarorin biyu ke yi.
A ɓangare guda, Kungiyar Tarayyar Afirka, na fatan tura wakilai zuwa Sudan, domin warware matsalar tsakanin shugaban soji General Abdel Fattah al-Burha, da tsohon mataimakinsa kuma kwamandan RSF, Mohamed Hamdan Dagalo.


