Ma’aikatar lafiya ta Hamas da ke Gaza ta ce kusan Falasɗinawa 400 aka kashe a Zirin Gaza cikin kwanaki biyu da suka gabata.
Hamas ta ce a jumulla mutum 390 ne suka mutu, wasu ƙarin 734 suka jikkata.
Tun bayan ɓarkewar rikicin ranar 7 ga watan Oktoba, ma’aikatar lafiyar ta ce fiye da mutum 200,000 aka kashe.
BBC ba ta iya tantance ikirarin yawan Falasɗinawan da suka mutu ba.


