Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce, jami’an tsaro sun samu nasarar kashe dukkanin manyan ƴan bindiga da ke kai hari a wasu sassan jihar.
Inda ta ce hakan ya sa a yanzu manoma sun samu damar fita gonaki domin yin noma fiye da lokutan baya.
Kwamishinan watsa labarai na jihar Alhaji Yakubu Ahmed Birnin kebbi ne ya bayyana hakan a cikin wata hira da BBC.
Sai dai a cikin hirar kwamishinan watsa labaran ya fara ne da bayyana irin nasarorin da ya ce gwamnan jihar ya samu a cikin shekara ɗaya kan Mulki.


