Sojojin kasar nan sun kashe wani dan ta’adda mai suna Buharin Yadi, daya daga cikin manyan ‘yan bindiga da ake zargin suna ta’addanci a Arewacin kasar nan cikin shekaru goma da suka gabata.
Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a yau Alhamis, cewa dakarun rundunar na ‘Operation Whirl Punch’, sun yi ruwan wuta a sansanin wanda ya yi sanadiyar hallaka Buhari Alhaji Halidu wanda aka fi sani da Buharin Yadi tare da ‘yan tawagarsa.
A cewarsa, an kawo karshen Buharin Yadi da tawagarsa wanda ke da alaka da sauran kungiyoyin ta’addanci da ke kashe mutane a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
A wani samame na daban kuma, dakarun sojin Najeriyar tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindiga da maɓoyar ‘yan ta’adda a kusa da Irele da Igbobini da kuma Segbemi Kiribo a yankin dajin Ese-Odo a karamar hukumar Irele ta jihar Ondo.
A yayin aikin share fagen, sojojin sun kwato bindigogi da makamai da dama.