fidelitybank

An kashe aƙalla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Date:

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan nan ya nuna cewa, cikin shekaru biyu da gwamnatin Tinubu ta hau mulki, an kashe aƙalla mutum 10,217 a hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a jihohi daban-daban.

Jihohin sun haɗa da Benue da Edo da Katsina da Kebbi da Plateau da Sokoto da Zamfara.

Jihar Benue ce ke da mafi yawan adadin mutanen da aka kashe – inda ya kai har mutum 6,896, sai Jihar Plateau da mutum 2,630.

Amnesty International, wadda ta fitar da wannan rahoto a cikar shekaru biyu na shugaban Najeriya, Bola Tinubu kan ƙaragar mulki ta zargi gwamnatinsa da gazawa wajen kare rayukan ‘yan kasa da kuma gurfanar da waɗanda ke da hannu a aikata laifuka duk da alkawurran da gwamnatin ta sha yi na inganta tsaro.

Rahoton ya kuma bayyana cewa “an raba ɗaruruwan ƙauyuka da muhallansu musamman a Zamfara da Benue da Plateau, inda dubban mutane suka rasa matsugunansu.”

“Hare-haren sun kuma lalata ababen more rayuwa da suka haɗa da rijiyoyin burtsatse da makarantu da asibitoci wanda hakan ya kara tsananta halin da jama’a ke ciki.” rahoton ya ƙara da cewa.

Amnesty International ta gargadi cewa korar manoma daga gidajensu na kara haddasa yunwa da talauci.

A jihar Plateau, an bayyana cewa mutum 65,000 ne suka rasa matsugunansu, a Benue kuwa adadin ya kai 450,000.

“Sababbin ƙungiyoyin ‘yan bindiga da suka hada da Lakurawa a jihohin Sokoto da Kebbi, da Mamuda a Kwara, na kara tsananta rikici.” in ji rahoton

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati da ta dauki matakan gaggawa domin dakile irin waɗannan hare-hare da kisan gilla, tana mai cewa “lokaci na kurewa, yayin da hare-haren ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya ke kara tsananta.”

sani ahmad

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Rikicinta da Cambodia na iya rikidewa ya koma yaƙi – Thailand

Thailand ta gargaɗi cewa rikicinta da Cambodia na iya...

Isra’ila da Amurka sun soki Faransa na amincewa da kafuwar ƙasar Falasɗinawa

Isra'ila da Amurka sun yi Allah-wadai da matakin da...

Najeriya za ta kwashe ma’aikatan ta a Congo – Tugar

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, ta na shirin kwashe...

Ministan harkokin jin ƙai ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa

Ministan harkokin jin kai, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya zama...

Amurka za ta lalata magungunan takarar haihuwa na dala miliyan 10 da za a kawo Afrika

Gwamnatin Amurka na shirin lalata magungunan tazarar haihuwa da...

Hukumar NAFDAC ta kama abubuwan fashewa a Kano

A cewar hukumar, an gano lita 60,000 na sulphuric...

Sojoji sun fafata da da ‘yan Bindiga a Neja

Rundunar sojiji ta ce, sojoji tare da haɗin gwiwar...

Majalisar Dinkin Duniya za ta dakatar da tallafin abinci a Najeriya

Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya bayyana...

Tinubu ya na murkushe ‘Yan adawa – Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ce...

Gwamnatin Kano ta baiwa yara fifiko – UNICEF

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya...

Majalisar ta amince da buƙatar Tinubu na ciyo bashin dala biliyan 21

A ranar Talata ne majalisar Dattawa ta amince da...

An sallami Gwamnan Katsina daga asibiti bayan ya samu rauni a hatsarin mota

An sallami gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda,...
X whatsapp