Gwamnatin Amurka ta tabbatar da mutuwar ‘yan ƙasarta tara a Isra’ila.
Cikin wata sanarwa Fadar White House ta ce ” muna miƙa ta’aziyyarmu ga waɗanda abin ya rutsa da su da muka iyalansu, kuma muna fatan waɗanda suka jikkata za su warke da wuri.”
“Kuma za mu ci gaba da bibiyar wannan lamari kuma mu ci gaba da tattaunawa da abokanmu na Isra’ila, musamman hukumominsu.”