Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kashe wani dan sanda mai suna Sule Babur a jihar Yobe.
Lamarin ya faru ne a gidan Babur da ke unguwar Mairi, Buni Yadi, karamar hukumar Gujba.
Bayan kashe Babur, maharan sun banka wa gidansa wuta, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim ya bayyana.
“Masu aikata laifin sun kuma kona gidansa. Lamarin da ya jefa al’umma cikin fargaba, kuma ana bukatar a gudanar da bincike cikin gaggawa domin gurfanar da masu laifin a gaban kuliya,” in ji Abdulkarim.