fidelitybank

An kashe ƴan Bindiga sama da dubu 13 a mulkin Tinubu

Date:

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa dakarun ƙasar sun kashe ‘ƴan ta’adda da masu aikata ta’asa a ƙasar sama da 13,543 a yankin arewa maso gabashin ƙasar tun bayan hawan shugaban ƙasar kan mulki kimanin shekara biyu da suka gabata.

Hakan na ƙunshe ne a cikin rahoto kan nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu a ɓangaren tsaro, wanda mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya bayar a ranar Talata.

Haka gwamnatin ƙasar ta bayyana cewa an ƙwato tare da lalata makamai sama da 11,118 a tsakankanin lokacin a yankin na ƙasar.

Ribadu ya ƙara da cewa iyalan ƴan Boko Haram da ISWAP sama da 124,408, sun miƙa wuya, sannan an ƙwato alburusai sama da 252,596.

Yankin arewa maso gabas dai ya ƙunshi jihohin Borno da Adamawa da Yobe da Bauchi da Gombe da Taraba, kuma yanki ne da ya shafe sama da shekara 10 yana fama da rikice-rikicen Boko Haram wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane, tare da raba miliyoyi da muhallansu

assu update

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...

Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan Mutane 3

Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin...

Ƴansanda sun kama ƙasurgumin ɗanbindiga a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce, jami'an ta sun...

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...
X whatsapp