Rundunar ‘yan sandan jihar Legas a ranar Litinin, ta tabbatar da kisan wani dan sanda a yankin Ikorodu da ke jihar Legas da wasu da ba a san ko su wanene ba suka yi.
Maharan sun tsere da bindigar dan sandan da aka kashe.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN cewa, wasu ‘yan sanda uku sun samu munanan raunuka a harin.
Jami’an rundunar ‘yan sanda reshen Imota da ke yankin Ikorodu suna aikin sintiri ne a lokacin da maharan suka kai hari a mahadar Emuren da ke kan titin Itokin a yankin.
Majiyoyin cikin gida sun ce maharan wadanda ake zargin ’yan fashi ne, sun yi wa tawagar ‘yan sandan kwanton bauna, inda suka bude wuta tare da kashe daya a nan take suka tsere da bindigarsa.
“A ranar Asabar ‘yan sanda sun kai farmaki maboyar ‘yan kungiyar asiri a Emuren, karamar hukumar Shagamu ta Ogun,” inji wani mazaunin garin.
NAN ta ruwaito cewa, mutane da dama da ba su ji ba ba su gani ba sun fada cikin hare-haren bindiga da jami’an ‘yan fashin suka kai a Ikorodu da kewaye a baya.