fidelitybank

An kashe ƴan bindiga tare da kuɓutar da mutane a Sokoto

Date:

Rundunar sojiji ta ce, ta kashe wasu ‘yan bindiga tare da kuɓutar da wasu mutane da suke garkuwa da su a jihar Sokoto.

Cikin wani saƙo da rundunar sojin ƙasar ta wallafa a shafinta na X, ta ce cikin wani hari da dakarunta na Hadarin Daji suka ƙaddamar a ƙauyen Bauni da dajin Bauni a jihar ranar 14 ga watan Disamba, inda sojojin suka shafe sa’o’i masu yawa suna musayar wuta da ‘yan bindigar.

Sanarwar ta ce bayan da sojojin suka matsa wa ‘yan bindigar, sai suka tsere tare da barin maɓoyarsu, lamarin da ya sa sojojin suka samu nasarar kuɓutar da mutum shida da suke garkuwa da su.

”Sai dai kafin tserewar ‘yan bindigar, sojojin sun kashe uku daga cikinsu, tare da gano makamai”, in ji sanarwar.

Makaman da aka gano sun haɗar da bindiga ƙirar AK-47 biyu da kuttun adana alburusai 19, da alburusai, da bindigogin toka biyu d babura, da na’urorin oba-oba da sauran kayayyaki

Sanarwar ta ce sojojin sun lalata maɓoyar ‘yan bindigar tare da babuwarn da suka gano nan take.

nnnnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp