fidelitybank

An kasa shayo kan ma’aikatan wutar lantarkin Kaduna

Date:

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna Electric da ke da alhakin samar da lantarki ga jihohin Kaduna da Kebbi da Sokoto da Zamfara ya ce an gaza cimma matsaya tsakanin shugabanninsa da kungiyar ma’aikatan kamfanin duk da sanya bakin gwamnati da masu ruwa da tsaki.

Babban Jami’in sadarwar kamfanin, Abdulazeez Abdullahi a cikin wata sanarwar da ya fitar, ya ce duk da Æ™oÆ™arin samun matsaya tsakaninsu, ma’aikatan sun Æ™i amincewa su maido da wutar lantarki bayan katse ta tun ranar Litinin 3 ga watan Fabrairu.

Ya ce an gudanar da taruka tare da hukumomin tsaro da Gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagoranci gwamnan jihar Uba Sani wanda mataimakiyarsa Hadiza Balarabe ta wakilta, inda ta bayyana yadda rashin wutar ke shafar fannin lafiya da kasuwanci ta kuma buƙace su da su mayar da wutar a lokaci ba tare da ɓata lokaci ba a lokacin tattaunawar.

A cewar sanarwar, an kuma yi zaman shiga tsakanin tare da babban lauyan Najeriya Sani Katu da kuma kwamishinan shari’ah na jihar Kaduna Sule Shuaibu SAN, sai dai haÆ™ar ta gaza cimma ruwa sakamakon sabbin buÆ™atu da Æ™ungiyar ma’aikatan ta gabatar.

Abdulazeez ya kuma ce: ”Wannan mataki da suka É—auka ya saÉ“a wa tabbacin da suka bai wa gwamnatin jihar Kaduna tun da farko na cewa za su mayar da wutar lantarkin a yayin da ake cigaba da tattaunawa.”

A farkon makon nan ne dai Kamfanin rarraba wutar lantarkin na Kaduna Electric ya ce ya sallami ma’aikata fiye da É—ari huÉ—u, wanda hakan ya kai ga shiga yajin aikin ma’aikatan tare da jefa alummomin jihohi huÉ—u cikin duhu.

Lamarin ya jefa al’umma cikin Æ™unci da haifar da asara ga masu sana’o’i.

mmm.nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp