Rundunar ƴan sanda reshen Jihar Katsina, ta karrama ɗan sanda mai suna Nura Mande, bayan ya gano dala 800 kuma ya mayar wa mai kuɗin a jihar Katsina.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun yan sandan reshen Jihar Katsina SP Gambo Isah ya aiko wa BBC, ɗan sandan mai muƙamin Constable ya samu kyautar naira dubu 30 daga kwamishinan ƴan sandan jihar bisa ƙoƙarin da ya yi haka kuma ya ba shi takardar karramawa.
Tun da farko dai Nura Mande ya ga kuɗin ne dala 800 kimanin Naira 480,000 a sansanin Alhazai na jihar a lokacin da yake aikinsa, kuma kuɗin na ɗaya daga cikin maniyattan da ke sansanin ne.
Kwamishinan ƴan sandan Jihar Katsina CP Idrisu Dabban Dauda ya jinjina masa, bisa wannan ƙoƙari da ya yi inda ya ce, Constable Mande ya nuna gaskiya da kima da kishin ƙasa wanda za a iya koyi da shi.