Rundunar soji ta musamman da ke da alhakin wanzar da zaman lafiya a jihar Filato ta karrama jami’an ‘Operation Safe Haven’ guda takwas, bisa kin karbar cin hancin Naira miliyan 1.5 daga wasu da ake zargin barayin shanu ne a jihar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, Kaftin Oya James ya fitar, ya ce jami’an 8 da aka tura sashin OPSH ta 4, sun kama wasu barayin shanu 30 na wani Shehu Umar a shingen binciken Bisichi da ke karamar hukumar Barkin Ladi a jihar.
Ya kara da cewa an yi awon gaba da shanun ne a garin Mangu kuma ana kai su zuwa wani wuri da ba a bayyana ba, yayin da dakarun rundunar da ke aikin tsagaita wuta suka tare su.
A cewar sanarwar, “wadanda ke cikin motar, Anas Usman dan shekara 20, da Gyang Cholly mai shekaru 42, nan take suka tunkari sojojin da nufin ba su cin hanci da rashawa tare da tabbatar da tsaron shanun da aka sace.
“An ki amincewa da neman kudin kuma an kama wadanda ake zargin, da kuma kudin da aka bayar na cin hanci.”
A cewar sanarwar, kwamandan rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo Janar Abubakar, yayin da yake mika kyautar kudi ga manyan jami’an, ya bukaci sauran jami’an tsaro da su ci gaba da nuna kyakykyawan hali da jajircewa wajen sauke nauyin da aka dora musu.
“Shugaban ma’aikatan OPSH, Brig. Gen. M.O. Agi, kwamandan ya kuma umarce su da su yi koyi da kyawawan halaye na ma’aikatan takwas,” in ji sanarwar.