fidelitybank

An karkare taron sauyin yanayi na kasar Masar

Date:

An Karkare babban taron sauyi yanayi na Majalisar Dinkin Duniya mai taken COP27, a kasar Masar ba tare da cimma matsaya kan rage gurbataccen iska ba, ko da yake an amince da ware kudade domin baiwa wasu kasashe su yaki dumamar yanayi.

An kammala Tattaunawar da aka shafe makonni biyu ana yi a wani wurin shakatawa na Sharm el-Sheikh dake kasar Masar, a ranar Lahadi tare da kulla wata muhimmiyar yarjejeniya kan bayar da kudade domin taimakawa kasashe masu rauni su tinkari mummunan tasirin yanayi, amma aka watse ba tare da cimma matsaya wajen rage garbatattacen hayaki da ake fitarwa ba.

Ministan yanayin Pakistan Sherry Rehman ta ce, bayan shefe sama da shekaru 30 ana gwagwarmaya daga karshe taron ya saurari koken kasashe marasa karfi wajen shere musu hawaye, wanda ke zama babban nasara da aka samu a Sharm el-Sheikh.

Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana farin cikinsa dangane da ci gaban da aka samu na samar da asusun asara da barnar tasirin sauyin yanayi, to sai dai kuma ya nuna damuwa kan gazawa wajen daukar matakan gaggawa na kawar da iska mai haifar da dumamar yanayi.

Matakin da Franministan Burtaniya Rishi Sunak ya yi gargadin cewa “dole sai an kara azama, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ba da shawarar sake wani taron a Paris domin amincewa da “sabon yarjejeniyar kunshin tallafin kudi” ga kasashe masu rauni gabanin taron na COP28 da za’a yi a Dubai na hadeddiyar daular larabawa.

vanguard news nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp