Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Kaduna ya sanar da karin farashin wutar lantarki ga masu amfani da layin wuta ta Band A wanda suke samun wutar lantarki na awanni 20 zuwa 24 a kullum.
Kamfanin ya sanar da hakan ne ta hannun shugaban sashen yada labarai na kamfanin, Abdulazeez Abdullahi ya fitar ranar Laraba.
Ya ce farashin kudin ya karu zuwa Naira 209.9 kan kowace kilowatt maimakon Naira 206.80.
Wannan shi ne karo na biyu da disco ke bayar da sanarwar karin kudin wuta ga abokan huldarsa na band A, bayan karin kudin wutar na ranar 3 ga watan Afrilu.
Idan za a iya tunawa, a ranar 3 ga Afrilu, Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta kasa, ta amince da karin kudin wutar lantarki da kaso 245 zuwa Naira 225 a kowane kWh daga Naira 68.