An kammala karɓar sakamakon zaɓen Adamawa daga ƙananan hukumomi 10, bayan ci gaba da aikin tattara sakamakon ranar Talata.
Su ne cikon ƙananan hukumomin da suka rage kafin INEC ta ɗage aikin karɓar sakamakon a ranar Lahadi.
Matakin ya zo ne bayan wai taro da kwamishinonin zaɓe na ƙasa suka gudanar bayan INEC ta gayyaci duk masu ruwa da tsaki a zaɓen cike-giɓin da aka yi ranar 15 ga watan Afrilu.
A yanzu kuma jami’in tattara sakamakon zaɓen, ya fara aikin shigar da alƙaluman cikin takardu, domin bayyana wanda ya yi nasara a zaɓen nan gaba.