A hukumance an kammala jefa ƙuri’a a zaɓen gwamna da ake gudanarwa a Jihar Osun.
Tun da farko hukumar INEC ta sanar da cewa za a soma tantancewa da kuma jefa ƙuri’a 8:30 na safe a kammala 2:30 na rana.
Tuni aka kammala kaɗa ƙuri’a a wasu rumfunan zaɓe kamar a rumfar zaɓe ta L.A. Primary School II da ke Otun Balogun a birnin Osogbo.
Rumfar zaben na da masu rajista 325, amma 138 aka tantance da na’urar BVAS don kada kuri’a.