An kammala bikin al’adun gargajiya daake yi wa lakabi an Rigata da aka saba gudanarwar a kowace shekera a masarautar Yauri da ke jihar Kebbi.
Kwanaki uku aka dauka ana gudanar da bikin, wanda ake nuna amfanin gona da ake nomawa a yanki Yauri da irin wasannin gargajiyar al’ummar yankin.
Bikin ya samu haralartar gwamnan jihar Alh. Nasir Idris da sarki Yauri, Dr Muhammad Zayyanu Abdullahi (C.O.N) da sauran manyan mutane daga ciki daga wajen jihar.
A wannan bikin karon farko an kamo dorina da ranta, inda mai Martaba Sarkin Yauri ya bai wa gwamnan jihar kyautarta.