Jami’an tsaron (NSCDC) reshen jihar Neja, sun kama wani dalibi mai shekaru 18 da haihuwa, bisa zargin yunkurin yin garkuwa da shugaban College of Fisheries, New Bussa.
Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASC Nasir Abdullahi, ya fitar ranar Laraba.
Ya ce wanda ake zargin, wanda dalibin kwalejin ne, ya hada baki da wani mutum daya, wanda a halin yanzu, ya rubuta wasikar barazanar yin garkuwa da provost idan ya kasa biyan kudin fansa.
Sai dai Nasir ya ce wanda ake zargin bai bukaci wani adadi na musamman ba kafin jami’an tsaro su kama shi, kamar yadda NAN ta ruwaito.
Kakakin ya kara da cewa, nan take aka gurfanar da wanda ake zargin a gaban wata babbar kotun majistare kan laifuka biyu da suka hada da hada baki da kuma tsoratarwa.


