An kama wasu yara maza biyu ‘yan shekara 12 da laifin kashe wani mutum, Shawn Seesahai, ɗan shekara 19 da adda a Wolverhampton a watan Nuwamban bara.
Lamarin ya faru ne a filin wasa na Stowlawn da ke East Park.
Yaran da ba za a iya bayyana sunayensu ba, su ne mafiya karancin shekaru da aka kama da laifin kisa tun bayan tsare waɗanda suka kashe James Bulger a shekarar 1993.
A yayin shari’ar da aka yi a Kotun Nottingham Crown, yaran sun zargi junansu, amma alkalan kotun sun kama yaran biyu da laifin kisan kai.
Daya daga cikin wadanda ake tuhuma ya amsa laifinsa na mallakar adda “ba tare da kwakkwaran dalili ko doka ba”, yayin da ɗayan kuma ya musanta aikata wani laifi amma kuma an kama su duka da laifin kisa a ranar Litinin