An kama mutum biyu a Najeriya saboda zarginsu da yunƙurin lalata da wani ɗalibi ɗan Australiya da ya hallaka kansa.
Ƴan sandan Australiya sun ce matashin da aka kashe ya yi musayar hotuna da wani mutum ta intanet kafin ya soma yin baraza da kuma neman kuɗi a hannunsa.
Bayan wani bincike da aka yi, an gano mutanen biyu da ake zargi a Najeriya inda za su fuskanci shari’a.
Ƴan sanda sun ce ɗabi’ar tilastawa mutum tura hotuna ta hanyar yin barazanar tona masa asiri musamman a tsakanin matasa na matuƙar ƙaruwa.
Ba a fitar da bayanan yaron – shekarunsa da kuma inda yake zaune a New South Wales ba, an yi haka domin kare iyalinsa.
Ƴan sanda a New South Wales sun ce waɗanda ake zargin suna tilasta tura masu hotunan jikin mutum ɗin matasa ne kuma sun ce sun yi barazanar tura hotunan matashin ga abokanai da kuma yan uwansa idan har ya ƙi biyansu dala 330.
“Saƙonnin sun yi muni. Sun matsa wa yaron lamba ya biya kuɗin,” in ji babban jami’in ɗan sanda da ke yaƙi da laifukan intanet, Mathew Craft, kamar yadda ya shaida wa jaridar Sydney Morning Herald.
Yaron ya mutu ne ta hanyar kashe kansa a yammacin ranar da abin ya faru s shekarar da ta gabata.
Ƴan sandan Australiya sun yi aiki tare da takwarorinsu a Afirka ta Kudu da Najeriya wajen zaƙulo mutanen da ake zargi da aika-aikar a Najeriya.
An gano shaidar da ke nuna matasan biyu sun yi ƙoƙarin karɓar kuɗi a hannun mutane cikin wayoyinsu, a cewar jaridar ta SMH. An tuhume su da zargin tilasta wa yaron ɗan Australiya kwanciya da su ba mutuwarsa ba. In ji BBC.