‘Yan sanda a Fort Portal sun cafke wani dan Najeriya mai suna, Musa Oze, bisa zargin satar wayoyin hannu.
An kama Oze kuma an tuhume shi da Patrick Tumusiime, Bob Amanyire, da Mugenyi Hamidu dukkansu mazauna Fort Portal dake kasar Uganda.
Kamen nasu ya biyo bayan daya daga cikin wadanda aka sace wa wayar ta kai rahoto ga ‘yan sanda. Vincent Twesigye mai magana da yawun ‘yan sandan yankin Rwenzori ya ce ‘yan sandan sun yi amfani da kyamarori na CCTV kuma sun sami damar bin diddigin Tumusiime.
A cewar Twesigye, a lokacin da ake yi wa Tumusiime tambayoyi, ya jagoranci ‘yan sanda zuwa Amanyire, wani makanikin waya a Fort Portal wanda kuma ke sayar da wayoyi na hannu.
A nan ne ‘yan sanda suka gano Oze, wanda a cewar binciken ‘yan sandan, shi ne ke da hannu wajen karkatar da lambobin wayoyin da aka sace. A cewar ‘yan sanda, Amanyire ya gaza yin lissafin hannun jarin da ya kai har aka kama shi.
Rundunar ‘yan sandan ta ce tana kuma binciken yadda Oze ya shigo kasar da kuma yadda ya fara mu’amala da wayoyin hannu.
Rundunar ‘yan sandan ta lura cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa da barayi suka rasa wayoyi suna sha’awar sauya Sim Card dinsu ne kawai ba tare da kai rahoton sata ga ‘yan sanda ba wanda ya ce yana kawo cikas ga bincike.