fidelitybank

An kama ‘yan Najeriya biyu a Kenya da zargin kisan kai

Date:

Yan sandan Kenya sun kama wasu maza biyu yan Najeriya saboda zargin suna da hannu a kisan wata daliba.

Sun bayyana gaban kotu sai dai ba a kai ga tuhumarsu ba.

An gano gawar daliba Rita Wdaeni mai shekara 20 cikin ladejin shara a wani gida da ke Nairobi babban birnin Kenya ranar 14 ga watan Janairu.

Kisan gillar da aka yi wa dalibar dai ya fusata al’ummar Kenya.

Sai dai kokon kanta tare da wayarta da sauran kayayyakinta, sun bata.

Kisan gillar ya sa an yi ta kiraye-kiraye a kara daukan mataki domin magance cin zarafin da ake yi wa mata.

Wasu yan Kenya hudu suma suna tsare game da kisan da kuma wani mutum wanda yake tafiye-tafiye da takardar fasfon Mozambique inda kuma aka damke shi yayin da yake shirin barin kasar.

Yan sanda sun bayyana sunayen mutanen biyu da ake zargi da William Ovie Opia da Johnbull Asbor.

Mr Opia yana da fasfon Najeriya wanda wa’adin amfaninsa ya cika kuma Mr Asbor ya rasa nasa fasfon shekaru biyu da suka gabata, kamar yadda yan sanda suka ce.

Yan sanda sun kwace kayayyaki da dama daga gidan mutanen da ake zargi ciki har da wuka da karamar adda da ake zargin sun yi amfani da su wajen kashe dalibar jami’ar tare da sauya mata kamanni, kamar yadda kafofin yada labaran Kenya suka rawaito yan sanda da cewa.

Mr Opia ya fada wa masu bincike cewa ya sayi addar ta intanet domin kare kansa, in ji jaridar Nation mai zaman kanta.

An kama mutanen biyu a Ndenderu, wani gari kai nisan kilomita 20 daga Nairobi kuma kusa da wata madatsa inda yan sanda suka gano kokon kan da ake zargi na Ms Waeni ne tare da wayoyinta da wasu kayayyakinta da suka bata.

Zuwa yanzu dai iyalin Ms Waeni basu kai ga tantance ko kan nata bane.

Iyalanta, a makon da ya wuce, sun ce wadanda ke da hannu a aika-aikar sun bukaci a biya su 500,000 a kudin Kenya kafin su saki Ms Waeni duk da cewa sun halaka ta.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da kungiyoyin kare hakkin mata sun shirya zanga-zanga a fadin kasar domin nuna fushinsu kan karuwar kisan mata da cin zarafin da ake masu.

An samu karuwar rahotannin kisan mata tun farkon wannan shekarar. Wani bincike da aka yi a 2022 ya gano cewa akalla kashi 34 cikin 100 na mata sun fuskanci cin zarafi a wasu lokuta na rayuwarsu.

www.nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp