An kama wasu ‘yan fashi da makami hudu da suka kai hari tare da kashe wani Birgediya Janar, Uwem Udukwere a Abuja.
Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Benneth Igweh ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin da yake gabatar da wasu mutane da ake zargi a hedikwatar rundunar.
CP ya shaidawa manema labarai cewa karin wasu ‘yan fashin guda biyu wadanda har yanzu ba a kama su ba, sun gudu da bindigar Janar din mai ritaya.
Igweh ya bayyana sauran ‘yan fashin da ake nema ruwa a jallo, ya kuma bada tabbacin za a cafke su tare da taimakon sauran jami’an tsaro.
DAILY POST ta tuna cewa ‘yan fashi da makami sun kashe Janar Udokwere a ranar Asabar a gidansa da ke Estate Sunshine da ke Abuja.