Ƴan sanda a jihar California ta Amurka, sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi a cikin motarsa kusa da wani gangamin yaƙin neman zaɓen Donald Trump.
An bayar da belin mutumin wanda aka tsare a wani shingen binciken ƴansanda yankin Coachella.
Shugaban ƴansanda yankin Chad Bianco ya ce a yayin gudanar da bincike, an samu fasfo da dama masu sunaye da daban daban da kuma lasisin tuƙi masu ɗauke da sunaye daban-daban.
An dai kara tsaurara matakan tsaro a wuraren gangamin Mista Trump, bayan an yi yunƙurin kashe shi har sau biyu a baya bayan nan.