Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta ce, jami’anta sun kama wani da ake zargi da satar mota tare da gano wani dan fashi da makami a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Kaduna.
Hassan ya ce, “A ranar 27 ga Mayu, da misalin karfe 1830, jami’an mu sun samu labari daga wani Basamariye nagari.
“Wani mutum ya ruwaito cewa an nemi ya taimaka wajen karbar Lexus LX470 Jeep daga kanikanci.”
A cewarsa, da karbar motar ya yi zargin sata ne, kuma ba tare da bata lokaci ba ya kai rahoto ga ‘yan sanda.
Hassan ya ce bayan rahoton an gano motar tare da kawo ofishin ‘yan sanda na Magaji Gari da ke cikin babban birnin Kaduna.
“An gudanar da bincike, inda aka gano bayanan motar da ke dauke da sunan mai shi, tare da lambar wayarsa.
“Da aka tuntubi mai gidan ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga biyar ne suka kwace masa motar da bindiga a gidansa da ke Utako, Abuja,” inji shi.
Hassan ya kara da cewa ‘yan sanda sun gudanar da bincike tare da samun nasarar cafke wanda ake zargin mai suna Mubarak Kabiru daga Kano a kan hanyar Alkali, Kaduna.
Ya kara da cewa, “Binciken da aka yi a dakinsa da ke Otal din Ishacool, Kabala Doki, Kaduna, an gano wani ma’aikacin da ke hana sa-ido.”