‘Yan sanda a India sun ce sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan da aka yi wa fitacciyar ‘yar siyasar nan kuma tsohuwar mai yin TikTok Sonali Phogat.
An kama mutanen ne bayan sakamakon gwajin gawar da aka yi ya nuna cewa kasheta aka yi saboda an ga raunuka a jikinta.
Sonali Phogat, mai kimanin shekara 42 da haihuwa, ta kai ziyara ne birnin Goa, in da aka kasheta a ranar 22 ga watan Augustan da muke ciki. In ji BBC,
Rahotanni farko sun ce bugawar zuciya ne ya yi sanadin mutuwarta, to amma daga bisani da aka yi wa gawarta gwaji aka gano kasheta aka yi.
Dan uwanta dai ya bayyana wa ‘yan sandan da ke bincike sunan wasu mataimakanta biyu in da ya ce sun rinka yi mata barazana da wani hoton bidiyo da bata son a gani.
Ya ce, mutanen sun yi mata fyade daga bisani kuma suka kasheta, sannan suka sace mata abubuwa da suka hada da waya da kuma katunanta na cire kudi wato ATM.
Iyalan marigayiyar sun ce kafin kisan nata sai da ta kirasu suka yi magana kuma sun ji ta kamar akwai damuwa a tare da ita.


