fidelitybank

An kama wanda ake zargi da damfara ta hanyar POS a Ibadan

Date:

Wani mai zambatar masu sana’ar hada-hadar kudi ta POS da kuma masu sayar da kayayyaki, ta hanyar aikawa da sakon shigar kudi (alert) ta waya , na bogi, ya fada hannun ‘yan-sanda.

‘Yan-sanda sun damke Adewale Adesanya mai shekara 45, a jihar Oyo, tare da kwalaben barasa mai tsadar nan wato shamfen (champagne) guda hudu, wadda kowa ce kwalba ta kai naira 117,900.

Jaridar DailyTrust ta ruwaito cewa, mutumin wanda ya ce wani abokinsa ne da suke zambar tare ya koya masa, sun sayi kaya na miliyoyin naira ta wannan hanya, da suke amfani da wata manhaja a wayarsu.

Adesanya ya ce zambar da ya yi ta karshe da aka kamashi shi, ita ce ta naira dubu 185, da ya yi wa wani mai POS a Ibadan .

Da yake gabatar da mutumin ga maneman labarai, Kwamishinan ‘yan-sanda na jihar ta Oyo, Adebowale Williams, ya ce, jami’an ‘yan-sandan ciki ne suka kama mutumin da ke zaune a gida mai lamba 7, Tiitin Awosika, Old Bodija, Ibadan.

breaking news in nigeria today punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp