Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin wakilin jam’iyyar siyasa ne mai suna, Shehu Aliyu Patangi, dauke da sama da naira miliyan 25.9 a Kaduna, kudaden da ake kyautata zaton an ware su domin siyan kuri’un zaben cike gurbi da za a gudanar a jihar.
Rahoton jaridar Leadership ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin da misalin ƙarfe 3:30 na asuba s ranar Asabar a wani otel da ke kan titin Turunku, Kaduna, ta hannun jami’an ‘yan sanda tare da na DSS.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya tabbatar da cewa an gano jimillar kuɗi har ₦25,963,000 a wurin wanda ake zargin, waɗanda ake tunanin an tanada domin sayen kuri’u a mazabar Chikun/Kajuru.
Ya ce yayin bincike, Patangi ya amsa cewa kuɗin an tanada su ne domin zabe, inda ya nemi a yi masa sassauci.