Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, ta kama wani mutum mai shekaru 50 da haihuwa da laifin kera bindigogi a karamar hukumar Ringim da ke jihar.
DSP Lawan Shiisu, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ya tabbatar da hakan a Dutse ranar Alhamis, inda ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 16 ga watan Nuwamba.
“’Yan sanda a Ringim tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan banga na yankin sun kama matashin dan shekara 50 da ke zaune a kauyen Yandutsen Kawari wanda ya kware wajen kera bindigogi ga miyagu,” in ji Shiisu.
Ya kara da cewa binciken da aka yi a gidan wanda ake zargin an gano wata bindiga da aka kera a cikin gida da kuma bindigu guda biyu.
Shiisu ya kuma bayyana cewa wanda ake zargin ya amince da kera manyan bindigogi tare da sayar wa mutanen da bai iya tantancewa ba.
Kakakin ‘yan sandan ya tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin da zarar an kammala bincike.