A ranar Larabar da ta gabata ne ’yan kabilar Awka suka kama wani matashi mai matsakaicin shekaru bisa laifin kashe biri.
An san birai dabbobi ne masu tsarki a daukacin masarautar Awka, kuma ana kallon kashe su a matsayin wani abu na ibada.
‘Yan asalin Awka na da wani biki da aka sadaukar domin bautar gunkin Imo Awka, wanda ke da wurin ibada a yankin Amaenyi da ke garin.
A daukacin masarautar, ba wani abin mamaki ba ne a ga birai suna tsalle-tsalle a cikin wuraren mutane ba tare da tsangwama ba.
Mutumin da aka kama a ranar Laraba da laifin kashe dabbar, an gan shi a cikin wani faifan bidiyo da ya yi ikirarin cewa ya rayu a Awka tsawon shekaru 24, kuma yana sane da cewa mutanen Awka ba su yarda a kashe ko cin naman birai ba.
Ya bayyana cewa, ba da gangan ya kashe biri ba, a’a, ya tada tarko ne a cikin daji, yana fatan ya kashe sauran naman daji da za a yi amfani da shi wajen cin abinci, amma abin takaici, biri ne ya makale.
Ya ce: “Na san na aikata, don Allah kar ka kashe ni, amma za ka iya kai ni duk inda kake so.”
‘Yan asalin da ke yi masa tambayoyi daga baya sun ga wasu dalilai a tare da shi, kuma suka ce masa ba za a kashe shi ba, amma al’umma za su dauki matakin farantawa Ubangijin kasa rai saboda abin da ya yi don kauce wa abin da ya faru.
Ba a dai bayyana inda mutumin ya fito ba, ko kuma sunan sa.