fidelitybank

An kama mutanen da suke hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Borno

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta kama wasu mutane hudu da ake zargi da hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar.

Kakakin rundunar, Nahun Daso, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Maiduguri.

Ya ce an kama wadanda ake zargin ne da rike da buhu 70 na ma’adanai iri-iri da ake zargin monoxide ne.

A cewarsa, an kama wadanda ake zargin ne a ranar 24 ga watan Maris, tare da wata motar dakon man dizal guda daya, inda ya jaddada cewa dakarun bataliya ta 331 da ke karamar hukumar Bayo ne suka kama su tare da mika su ga ‘yan sanda.

Kakakin ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake zarginsu da shi, inda ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike.

Ya ce a karshen binciken za a gurfanar da su a gaban kotu.

Borno na da albarkatu masu yawa da suka hada da Feldspar, Limestone da Kaolin.

Sauran sun hada da Potash, Iron-Ore, Quarts, Magnetite, Diatomite, Trona, Mica, Silica Sand, Gypsum, Granite, Flutters Earth da Uranium, da sauransu.

vgn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp