An kama wasu masu kallon wasan ƙwallon ƙafa a Hong Kong bisa zargin cin mutuncin taken ƙasar China, bayan da suka ƙi tashi tsaye lokacin da aka sanya taken a filin wasa.
Mutanen, maza biyu da mace ɗaya sun je kallon wasan da Hong Kong ke yi da Iran ne, na neman gurbin zuwa gasar cin Kofin Duniya.
Ƴansanda sun ce mutanen sun kuma juya bayansu a lokacin. Kafofin yaɗa labarai na birnin sun ce an tura ƴansandan ciki ne filin wasan domin su riƙa duba ƴan kallo.
Sai dai daga baya an bayar da belin waɗanda aka kama.
Duk mutumin da kotu ta same shi da laifin cin mutuncin taken ƙasar China, zai iya fuskantar ɗaurin abin da ya kai shekara uku a Hong Kong.
An yi wannan sabuwar doka ne bayan da zanga-zangar gama-gari da aka yi ta yi ta rajin tabbatar da dumukuraɗiyya a Hong Kong.