An kama wasu mutane biyu da ake zargin sun kashe Sagir Hamidu, tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara, kuma mai makarantar Famak British Schools, in ji rundunar ‘yan sandan.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja.
Wadanda ake zargin sun hada da Sani Usman dan shekara 22 da Mohammed Tijjani mai shekaru 23 da haihuwa daga Pai Konkore, Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja, bisa laifin yin garkuwa da mutane da fashi da makami a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna. Yace.
Adejobi ya bayyana cewa, hukumar ta Force Intelligence Bureau Intelligence Response Team (FIB-IRT) ta kama wadanda ake zargin tare da wasu 21 da laifin kisan kai, fashi da makami, garkuwa da mutane, safarar makamai, mallakar haramtattun bindigogi, da fyade da sauransu.