fidelitybank

An kama mutanen da ake zargi da kashe Malamin Jami’ar Maiduguri

Date:

Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce, ta kama mutum takwas da ake zargi da hannu a kisan wani malami da ke koyarwa a sashen ilimin motsa jiki da ke jami’ar Maiduguri.

Kakakin rundunar ASP Daso Kenneth, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa waɗanda ake zargin an kama su ne bayan wani rahoto da babban jami’in tsaron jami’ar ya shigar.

A cewar kakakin, babban jami’in da ke gadin jami’ar ya kai rahoto ofishin ƴan sanda da safe cewa an ga wata gawa a ofishi wadda aka gano ta Dakta Abdulkadir Kamal ce.

Kakakin ya ƙara da cewa da samun rahoton, aka aike ƴan sanda zuwa wajen inda kuma aka kai gawar asibiti domin yin bincike a kanta.

Ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano mutanen da ke da hannu a aika-aikar duk da cewa sun kama mutum takwas da ake zargi suna da hannu a kisan malamin.

A nasa ɓangaren mai magana da yawun jami’ar, Farfesa Danjuma Gambo ya ce an halaka Dakta Abdulkadir a ofishinsa da yammacin ranar Lahadi.

www.legit.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp