Hukumar tsaro ta NSCDC a Najeriya reshen Jihar Nasarawa ta ce ta kama ɗan shekara 20, Haruna Muhammad, da zargin yi wa yarinya mai shekara 13 fyaɗe da yi mata ciki a Lafiya, babban birnin jihar.
NSCDC ta ce ta kama wasu mutum biyu daban da zargin lalata da wata ‘yar shekara 13.
Da yake gabatar da su a gaban ‘yan jarida, kakakin hukumar, DSC Jerry Victor, ya ce an kama mutanen ne a wurare daban-daban na jihar.
“Waɗanda ake zargi; Haruna Abdullahi mai shekara 39 ya fito daga Tudun Kofa, da Dauda Muhammed mai 35 daga yankin Dawaki, sun amsa laifinsu na yi wa Ramatu Dahiru mai shekara 13 fyaɗe a Tudun Kofa,” a cewarsa.
Ya ƙara da cewa Dauda Mohammed da ake zargi da yi wa yarinyar fyaɗe abokin mahaifinta ne.
Yarinyar ta shaida wa kafar yaɗa labarai ta Daily Trust cewa mutumin ya yi lalata da ita ne bayan ya kira da zimmar zai aike ta.