Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da yin barazanar yin garkuwa da wani dan kasuwa da iyalansa.
Kakakin ‘yan sandan DSP. Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
A cewar sanarwar “wani mai suna Dauda Adamu ‘m’ mai shekaru 52 a kauyen Zadau B/Kudu ya kawo rahoto a sashin B/Kudu cewa, wasu da ba a san ko su waye ba sun kira shi ta wayar tarho suka yi masa barazanar zai ba su kudi ko kuma su yi kasadar yin garkuwa da su tare da danginsa”
Ya ce bayan samun rahoton ne ‘yan sandan da ke aiki da sashin B/Kudu suka shiga aikin.
DSP. Shiisu ya ce bayan samun rahoton an kama wani Ahmed Audu daga garin Basirka da ke karamar hukumar Gwaram da kuma Adebayo Abayomi daga kauyen Ogigi karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi, aka kai su ofishin domin bincike.
A yayin da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa laifin aikata laifin, kuma an kwato katin SIM na lambar da aka yi amfani da su wajen kiran wadanda suka kai karar daga hannunsu.
An mika wadanda ake zargin zuwa SCID Dutse domin gudanar da bincike mai zurfi.