fidelitybank

An kama mutane biyar da zargin tsafi a Ogun

Date:

An kama wasu mutane biyar da ake zargi da aikata ayyukan tsafi a Ososa da ke karamar hukumar Odogbolu a jihar Ogun.

An kama wadanda ake zargin ne biyo bayan samun bayanan da ‘yan sanda suka samu a hedikwatar sashin Odogbolu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Karanta Wannan: Idan aka cigaba da kama mutanen mu zamu mamaye ofishin ‘yan sanda – PDP

Ya ce ’yan kungiyar da ke da alhakin tono gawarwaki a cikin al’ummar Ososa, sun shirya wani wuri a cikin garin domin sake yin wani zagaye na girbin sassan jikin dan Adam.

Da yake bayyana wadanda ake zargin Oshole Fayemi, Osemi Adesanya, Ismaila Seidu, Oseni Oluwasegun da Lawal Olaiya, kakakin rundunar ‘yan sandan ya zarge su da tono gawarwaki daga cikin kaburburansu tare da cire wasu sassan jikinsu domin yin ibada.

Oyeyemi ya kara da cewa a cikin sanarwar, wadanda ake zargin suna da shekaru daga 30 zuwa 60.

“Bayan samun labarin, DPO Odogbolu, CSP Godwin Idehai, ya tattara mutanensa tare da kutsawa maboyar wadanda ake zargin inda aka kama biyar daga cikinsu,” inji shi.

“A yayin da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun yi ikirari cewa a zahiri suna sana’ar tono gawarwaki ne daga kaburburansu kuma suna sayar da sassan gawar ga masu sayan su da ke bukatar ta domin neman kudi.”

Da yake mayar da martani kan kamun, kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, Frank Mba, ya bayar da umarnin a mika wadanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike mai zurfi tare da gurfanar da su gaban kuliya.

www.legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp