Rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti ta ce, ta kama mutum takwas da suka yi garkuwa da wasu ɗalibai da malaman makarantar Apostolic Faith a Emure-Ekiti, da ke jihar.
Kwamishinan ‘yansandan jihar CP Adeniran Akinwale, ne ya bayyana haka lokacin da yake holen masu garkuwar a shalkwatar rundunar da ke birnin Ado-Ekiti, ranar Juma’a.
Mista Akinwale ya ce an kashe ɗaya daga cikin masu garkuwar a lokacin musayar wuta da jami’an ‘yansanda.
Kwamishinan ya ƙara da cewa maharan su ne kuma suka yi garkuwa da shugaban jam’iyyar APC na jihar, Hon. Paul Omotoso a shekara 2023
”Binciken farko ya nuna cewa Sumo Karami, tare da yaransa ne suka sace tare da yin garkuwa da ɗaliban nan da malamansu a Emre-Ekiti ranar 29 ga watan Janairu”, in ji kwamishinan.
Ya ƙara da cewa “Mun gano wayar da masu garkuwar suka yi amfani da ita wajen kira domin neman kuɗin fansa don sakin ɗaliban da malaman a hannun maharan”.
“Haka kuma an gano wasu abubuwa tare da maharan, daga ciki har da bindiga ƙirar AK-47 da wata ƙaramar bindiga da harsasai biyar a cikinta, sannan kuma da abun kurtun AK-47 21 maƙare da harsasan, sa sauran abubuwa”, in ji mista Akinwale.


