fidelitybank

An kama mutane 8 da bindigu a Kano

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta kama wasu mutane takwas da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka addabi jihar da kewaye tare da kwato bindigogi kirar AK-47.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP ya sanya wa hannu Abdullahi Haruna Kiyawa.

Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a wani samame daban-daban da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gudanar tare da kungiyar ‘yan banga.

A cewarsa, “An fara gudanar da samamen na farko ne a ranar 03/09/2023 bayan da ‘yan sanda suka samu rahoto daga hakimin kauyen Getso Gwarzo, Kano, cewa wasu gungun ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun mamaye kauyen a kan babura.

“Wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wata mai suna Zaliha Idris da ke kauyen ‘Yar’aduwa a Jihar Katsina da babur din su mai suna Boxer mai launin ja.”

Ya kuma ce a wannan rana, wani Abdullahi Idris na karamar hukumar Baji Sumaila, Kano, wanda aka kama bisa laifin satar shanu da kuma kisan gilla, ya jagoranci tawagar rundunar ‘yan sandan wajen cafke wanda ya taimaka masa.

Ya bayyana cewa an kwato bindiga kirar AK-47 mai lamba Breech No: 35535 da kuma mujalla daya makil da alburusai goma sha hudu (14) na 7.6239.

Sanarwar ta kara da cewa, a ranar 29/09/2023, ‘yan sanda sun kai samame a maboyar masu garkuwa da mutane a dajin Dansoshiya, sun kama wani Kabiru Haruna tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda daya na gida.

Ya ce ana ci gaba da kokarin kamo wadanda ake zargin sun gudu, inda ya ce an gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP. Mohammed Usaini Gume ya bukaci dukkan jami’an ‘yan sanda na rundunar da su ci gaba da zage damtse wajen yaki da miyagun laifuka.

Ya kuma yabawa al’ummar jihar bisa yadda suke ci gaba da addu’o’i, goyon baya, fahimta, karfafa gwiwa da hadin kai wajen yakar miyagun laifuka da aikata laifuka a jihar.

the sun newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp