An kama wasu mutane 5 yayin da suke satar Man Fetur da ake kira Automotive Gas Oil, wanda aka fi sani da Diesel a jihar Ogun.
DAILY POST ta samu cewa wasu jamiāan So-Safe Corps reshen jihar Ogun ne suka kama wadanda ake zargin suna aikata laifin a wani kamfanin gine-gine da ke Siun a karamar hukumar Obafemi/Owode a jihar.
Kakakin rundunar So-Safe Corps, Moruf Yusuf, ya ce jamiāan rundunar da ke hedikwatar sashin Owode (Egba) ne suka cafke mutanen biyar da misalin karfe 8:30 na yammacin ranar Laraba, 20 ga watan Satumba.
Yusuf ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da Abdullah Mohamed (34), Lambo Lack (54), Joel Dawab (40), Wellplus Masua (54), da Seidu Ibrahim (20).
āAn kama wadanda ake zargin ne a wurin da aka aikata laifin, saboda suna satar Automotive Gas Oil (Diesel) na kamfanin gine-ginen hanya (an sakaya sunansa), kafin shiga tsakanin jamiāan So-Safe Corps da ke kare kamfanin.ā Yace.
Kakakin ya kara da cewa an kwato kwali takwas da kowannen su ya kunshi lita 30 na dizal din da aka sace daga hannun wadanda ake zargin.
An mika wadanda ake zargin da abubuwan baje kolin da aka samu tare da su ga āyan sanda da ke Owode Egba.