fidelitybank

An kama Mutane 327 masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a Najeriya

Date:

Gwamnatin tarayya ta ce, ta kama mutum 327 da ake zargi da aikin haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a faɗin ƙasar nan.

Ministan Ma’adanai Dele Alake ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a bikin cika shekara ɗaya da kafa rundunar kula da harkokin haƙar ma’adanai ta Mining Marshals (MM).

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito shi yana cewa, an kama mutanen ne tun daga kafa rundunar a 2024, inda ma’aikatarsa ta yi nasarar gurfanar da 143 daga cikinsu a gaban kotu.

Ya ƙara da cewa babban abin da suka saka a gaba a 2025 shi ne gurfanar da sauran mutanen a gaban shari’a.

An ƙaddamar da rundunar MM ne ranar 21 ga watan Maris na 2024, inda ta fara aiki da dakaru 2,220 kafin su ƙaru zuwa 2,670, a cewar NAN.

spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...
X whatsapp