fidelitybank

An kama mutane 30 a rikicin kona bankunan Ugun

Date:

Al’amura sun fara lafawa a karamar hukumar Sagamu na jihar Ogun bayan wani zanga-zanga da ya karaɗe garin da safiyar ranar Litinin kan ƙarancin man fetur da kuma sabbin kuɗi.

An far wa bankuna da wuraren kasuwanci tare da cinna musu wuta da lalata motoci, inda aka tilasta wa masu shaguna rufewa.

A cewar kwamishinan ‘yan sandan jihar, Frank Mba, wanda ya jagoranci jami’ansa da kuma sojoji zuwa wurin da lamarin ya faru, ya ce an kama mutum 30 waɗanda ake zargi da hannu a tayar da hankali.

Mazauna garin sun ce an soma tarzomar ne da mislai karfe 5:30 na safe lokacin da akasarin mutane na barci.

Hanyoyi da lamarin ya shafi ya haɗa da titin Oba Erinwole, inda aka far wa rassan bankuna kusan bakwai da kuma lalata na’urorin cirar kuɗi na ATM, abu kuma da ya kassara illahirin garin.

Karanta Wannan: An kama matasa a Delta da suka yi wa Banki rotse

Gidan talabijin na Channels, ya ruwaito cewa wasu ɓata gari sun fasa ginin wani banki, inda suka yi yunkurin shiga ciki domin aikata ta’asarsu.

Sai dai tawagar kwamishinan ‘yan sandan jihar ne tare da haɗin gwiwar sojojin Najeriya suka taka musu burki da kuma takaita yaɗuwar zanga-zangar zuwa wasu wurare a jihar.

nnnhausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp