Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wasu mutane uku da ake zargi da kashe shugaban karamar hukumar Bauchi, Hussain Gwabba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar SP Ahmed Wakil ya fitar.
Ya ce, binciken farko kan kisan da aka yi wa Gwabba ya kai ga kama wasu mutane uku da ake zargi.
“Ana jiran sakamakon binciken gawar, sakamakon binciken za a bayyanawa jama’a halin da ake ciki,” in ji kakakin ‘yan sandan.