Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin sace wani basarake, Abdulrahaman Ifabiyi, Onire na Owa-Onire, a karamar hukumar Ifelodun ta jihar a ranar Asabar da ta gabata da wasu mutane dauke da makamai suka yi.
Wadanda ake zargin: Bello Abubakar (31) da Bawa Seketri (30), ana tsare da su ne bisa zargin sace sarkin da matarsa da direban sa ranar Asabar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Okasanmi Ajayi, a wata sanarwa da ya fitar a Ilorin ranar Lahadi, ya ce wadanda ake zargin suna taimakawa ‘yan sanda wajen gudanar da bincike kan lamarin.
Okasanmi, ya ce kokarin ceton da rundunar ta yi ne ya sa aka sako matar sarkin kuma ta sake haduwa da iyalanta.
Ya ce ana ci gaba da kokarin kubutar da sarkin da direban sa a hannun masu garkuwa da mutane.
Okasanmi ya ce, kwamishinan ‘yan sandan, Paul Odama ne ya aike da tawagar ‘yan sandan dabarun yaki tare da ‘yan banga da mafarauta zuwa yankin nan take, tare da ba da umarnin kubutar da wadanda abin ya shafa tare da kamo wadanda suka aikata laifin.