Kimanin mutane 19 da ake zargin sun wawure wata motar shinkafa a ranar Lahadi a Kano sun shiga hannun jami’an hukumar tsaron farin kaya ta NSCDC reshen jihar Kano.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan DSC Ibrahim Idris-Abdullahi, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun kai harin ne a kan hanyar Kano zuwa Zariya.
A cewarsa, motar da ke dauke da daruruwan buhunan shinkafa mai nauyin kilogiram 50 daga kamfanin Alhamsad Rice Mill da ke Sharada a Kano, tana da rajista mai lamba UGG 532 XA.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun far wa motar ne suka yi awon gaba da buhunan shinkafa, inda ya jaddada cewa motar ta nufi Zariya a jihar Kaduna.
DSC Ibrahim Idris-Abdullahi ya ce, “Da samun rahoton, jami’an NSCDC sun yi gaggawar tura jami’ansu zuwa wurin, inda suka kama wadanda ake zargin sannan an kwato musu buhunan shinkafa 29.”
Ya ce an kubutar da direban babbar motar da mataimakansa ba tare da wani rauni ba, yana mai tabbatar da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.